Posts

Showing posts with the label ISLAM

TAMBAYOYI 106 GA 'YAN MATA DA MATAN AURE ?

TAMBAYOYI 106 GA 'YAN MATA DA MATAN AURE ?
MATSALOLIN JININ HAILA DA NA ISTIHALA NO:1 YAYA AKE GANE JININ HAILA ? AMSA
Jinin haila Shi wani jine ne baki mai kauri mai wari wanda yake gudana da kansa daga gaban mace a wadansu lukuta sanannu ba tare da wani dalili na ciwo ko haihuwa ba.


{sahihu fiqhu Al-sunnah p:178


NO:2


YAYA AKE GANE JININ BIKI ?


AMSA

Shi wani jini ne mai fitowa a sababbin haihuwa.{Sahihu Fiqhu Al'sunnah p:186N0:3


YAYA AKE GANE JININ IS'TIHALA {JININ CIWO} ?AMSA


Shine zubowan jini daga gaban mace ba a lukutan haila ko biki ba ko kuma bayan karewan kwanakinsu. Shi jini ne wanda baya cikin dabi'ar mata ko halittar su, abin sani wata jijiya ce ta yanke wanda jini jajur yake kwarara baya yanke wa face an nemi magani.{Sahihu Fiqhu Al'sunnah p:187}

MANUFAR AIKIN DAN AGAJI

Image
Manufar aikin dan agaji

Aikin Dan Agajin shine bada taimakon farko ga majinyaci nan take kafin akaishi ga likita. Hade da taimakawa al'umma baki daya musulmai da wadanda ba musulmai ba musamman a wajen tarukan addini da harkokin tsaro a afadin nigeria.


Bada taimakon farko shine manufar aikin Agaji Ga dan agaji, Fareti baya daga cikin aikin agaji, sai dai akanyi shi domin motsa jiki ga dan agaji. 'Yan agajin Izala wadanda Eng. Mustapha Imam Sitti yake jagoranta suna da horo na aikin agaji, basa rike sanda ko wani katako mai kirar bindiga domin fareti Ko Motsa jiki, musamman ganin yadda harkokin tsaro suka zama a kasa.


Dan haka Daraktan agaji na kasa, Eng Mustapha Imam sitti, ya murci daraktocin agaji na jihohi, da wakilan agaji na kasa a jihohin Su, da su kula da irin masu daukan sanda suke fareti, wannan kungiya ta haramta hakan a tsarin faretin yan agaji domin kaucewa jefa mutane a rudani.


Allah ya taimake mu.